Reader mode
Kwai acikin kaya book 1 Chapter 18
4,500 words
Ba a wani ɗauki lokaci mai tsawo ba Aliyu ya shigo Office ɗin, lokacin Jawaad na tare da Rose suna magana akan wani aiki daya sakata. Zama Aliyu yayi a kujerar dake kallon ta Rose ɗin ya miƙama Jay takardu na results ɗin, ya kuma ajiye kwalaben dake a ledar. "Boss Result biyu fa yayi kama da na farko, dan a jikin syringe ɗin jiya yatsun hannun mutum biyu muka samu, amma ɗaya yafi fitane da ƙyau, duk da dai haka mun samu yanda mukeso. Ka duba da Result ɗin jiya da waɗannan na saman na mutane biyune dake jikin syringe ɗin kamar yanda na faɗa maka tun farko". Kai Jay ya shiga jinjinawa yana ɗan lila kansa a kujera, tuni idanunsa sun canja launi sai wani munafukin murmushi dake shimfiɗe bisa fuskarsa wanda Aliyu da Rose duk suka kasa fahimta. Cikin sauke numfashi ya ajiye takardun yana maida kallonsa ga Aliyu. "Aliyu kiramin Jabeer". "Okey Boss" Aliyu ya amsa yana ƙoƙarin kiran Jabeer a waya, koda Jabeer ya ɗaga daga can sai Aliyu ya sanar masa saƙon Jawaad. Babu jimawa kam saiga Jabeer ɗin. Jawaad dake rubutu a takarda ya ɗago ido ya kalli Jabeer, kafin ya miƙa masa takardar daya gama rubutun. "Jabeer wannan Number ɗin nakeson nasan daga shekaran jiya zuwa yau da mutum nawa akai waya, sannan mutane nawa suka kira layin?". Amsa Jabeer yayi yana kaɗa kai, ya nufi wasu Computers guda uku dake can gefe a cikin Office ɗin Jawaad. Hakan ne ya saka Aliyu miƙewa yabi Jabeer dan ya taimaka masa. Rose ma mikewar tai ta koma wajen su Jabeer ɗin, shiko Jawaad ya cigaba da aikin da yake a Computer gabansa zuciyarsa na masa wani zogi da ƙuna, domin kuwa result ɗin sayin hannun Jack da Shahudah aka samu a jikin syringe ɗin, na Jack shine ya danne na Shahudah alamar shine ƙarshen riƙe sirinjin. Kusan mintuna goma sha biyar Jabeer ya juyo yana kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga aikinsa tamkar babu abinda ke damunsa. "Boss ga waɗanda sukai kiran da waɗanda aka kira, sai text messages guda uku da akayi, kuma duk a jiyane kamar ma kai akaimawa". Miƙewa Jawaad yay zuwa inda su Jabeer suke, Aliyu yay saurin tashi ya bashi kujerar da yake zauna, jawota baya kaɗan Jay yay ya zauna, da kansa duk yabi ya duba, tabbas saƙo biyu shi Shahudah ta turomawa, sai dai babuma wanda ya duba a ciki dukda yaga shigowarsu tun ɗazun da safe, komawa yay duba Numbers uku da Shahudah ta kira randa abun ya faru, ya ƙurama Number ƙarshe ido yana nazarinta. Kallon Rose dake tsaye yay yay mata nuni data ɗakko masa wayarsa dake tebir ba tare da yay magana ba. Cikin hanzari taje ta ɗakko ta kawo masa. Number Aamilah da tunda yake bai taɓa kiraba sai dai ita ta kirashi ya lalubo. Akan laɓɓansa ya furata, "Aamilah" a hankali, Murmushi ya saki yana cizar leɓensa na ƙasa, "Jabeer bincikamin itama wannan Number " yay maganar yana nuna masa Number Aamilah. itama duƙufa Jabeer yay a kanta, ana cikin hakane Hafiz ya shigo hannunsa ɗauke da takardu, ganin sun haɗa kai waje guda ya nufisu yana faɗin, "Wane shagalin ake anan kuma?". Duk kallonsa sukayi, banda Jawaad da Jabeer da hankulansu ke bisa Computer ɗin. Jabeer yace, "Wannan sune ta kira a jiya, waɗan nan suka kirata, ga kuma na yau". Shiru Jawaad yay yana kallon Numbers ɗin, ya sauke numfashi yana girgiza kai, "Ina na shekaran jiya?". "Gasu nan" cewar Jabeer yanama Jawaad nuni dasu bayan ya kuma zooming ɗinsu yanda Jay zai gani sosai. Ahankali ya ringa nazarinsu ɗaya bayan ɗaya, "Jabeer inason nasan kowacce number daga ina akai kira da ita, wanda ta kura kuma a ina yake". "Amma zamu ɗauki lokaci Boss, magriba kuma ta gabato........" Kafin Jawaad yay magana Rose tace, "Bara muyi tanan kawai zaifi mana sauri". Duk juyawa sukai suna kallonta har Jay ɗin da yake lafe jikin kujera yana shafa ƙasumbar data ɗan taru mai a fuska kaɗan. Sun santa mayyace itama a irin waɗannan binciken, shiyyasa suke son zamanta a tafiyarsu sosai. Tana danne-danne tana kai kawo, hakan yasa suketa binta da kallo, shima Jabeer bai fasaba dubawar yake daga ɓangarensa. Cikin min tunan da basu gaza biyarba, Rose tace, "Number mai ƙarshe 3434 mai ita tana a anguwar Sunusi Abdullahi stress, layi na biyu gida mai lamab 107, an kiratane da ƙarfe 10:34am, zamu iya kiran kamfanin layin idan kana bukatar jin abinda aka tattauna akanta Boss". Cikin kafeta da idanu yace, "Kin tabbatar?". "Yes Sir, gashima ka duba da kanka" tai maganar tana miƙa masa. Amsa yay shima yana dubawa, duk abinda ta faɗa dai-dai ya gansa, wani luuuu yay da idanunsa yana busar da huci mai azabar zafi. Kafin ya samu cewa wani abu Jabeer ya katseshi da faɗin, "Boss ita kuma wannan daga Asibitin *NASARARMU* yanzu haka ma mai Number yana cikin asibitin, sannan Number da Rose take magana itama ta kirashi mintuna biyar kafin ita wannan ta kirasan, shima kuma ya kira waccan ɗin bayan awa ɗaya da kiran wannan. Da ƙarfi Jawaad ya bugi tebirɗin da Computers ɗin suke kai, sai faman fidda numfashi yake da sauri-sauri. Cikin kakkausar murya yace, "Muna idar da salla ku tababbar likitannan ya gurfanu a gabana, sannan mai wannan number itama kuje har gidan ku kamomin ita!!!". Ya ƙare maganar a matuƙar tsawace. Su duka a tsorace syke kallonsa, gashi dama basu san komai game da aikinba, amma sun kula ya ɗaukesa da zafi tun jiya. A cikin girmamawa duk suka amsa masa. Uffan bai sake faɗaba, sai da ya ɗauki rigar suit ɗinsa yana nufar ƙofa yace, "Duk ku kaimin su Zangina road ina jiranku a can". Bai jira amsarsuba yay ficewarsa...............🤫✍🏻
Naji dukkan ƙorafinku akan son posting kullum, sai dai nace kuyi haƙuri kam, dan lokacine banda shi isashe, buks biyu nakeyi a lokaci guda, bazai yuwu kullum nace zan fidda pages biyu ba, na farko typing yana lashe lokutane, ga hidimar gida, sannan idanuna, ko bakwaso na tsufa da idanune😂?, sai kuma ita kanta ƙwalwa ai tana buƙatar hutu, ta hakanne za'a samu rubuta abu mai amfani da nutsuwa, sannu-sannu bata hana zuwa, da zaran mun kammala ZAFAFA komai zai dai-daita da izinin UBANGIJI, ngd da Comments ɗinku dan suna sani nishaɗi matuƙa, hakama addu'oinku ga mahaifina sukan ƙaramin jin kaimin muku typing koban niyyaba😭🙏🏻, I luv u wujiga-wujiga my kankanati fans😻😻🤫😂.
*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
Please and Please amana subscribing domin nuna ƙauna🤩🤝🏻
*_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*_____________________________________* *_BOOK ONE_* _Shafi na ashirin da bakwai_ *_____________________________________*
............Koda motar Jawaad da ta Security's nashi suka iso ƙofar gidan nasu Shahudah basu shigaba, cayay suyi fakin a ƙofar gida. Zamansa yay a mota bai fitaba, hakan yasa securitys nashi fitowa su zagaye motar da yake a ciki. Yanata danne-dannensa a waya kai kace bashi bane ya fito Office ɗazun a fusace, sai dai shi yanajin zafinne a cikin zuciyarsa, yayinda fuskarsa ta shanye komai tamkar babu komai. Har aka kira sallar isha'i suna wajen, da kansa ya buɗe ya fito daga motar dan son gabatar da salla. Masallacin anguwar dake jikin gidan maƙwaftan su Shahudah suka shiga, tare dasu akai jam'i, suka bar waɗanda basayi a wajen.
Bayan fitowarsu daga salla ne sai ga su Hafiz sun iso tare da Zaitun da Dr Jeo, sake shiga mamaki Zaitun tayi ganin ɗan uwanta Jawaad da take mutuwar ƙauna. Shiko kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tamkar bai santaba ma. Shi da rose da Hafiz, kawai suka shiga gidan, aka bar Aliyu da Jabeer a waje tare da securitys da su Zaitun da aka zubo a mota.
Amina data fito tana shirin wucewa gida tai azamar matsawa ta basu hanya jikinta na rawa, ko kallonta basu yiba kuwa, sai knocking ƙofar falon da Rose ta shigayi. Amina da ta samu waje ta laƙe inda zata kalli komai, tace, "Ai dama tunda naji dambarwar da akeyi ɗazun a gidan nasan yau akwai kura", dan haka tai azamar komawa ta ƙofar kicin ta baya, dan tayi alƙawarin sai taga komai kodan ta bama Bilkisu labari idan ta dawo.
Tunda labarin zuwan Dr Tayyeb wajen Jawaad yazoma su Shahudah kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye, ga Dad baya nan yayi tafiya jiya da yamma. Aamilah tafi kowa shiga ruɗani dan dama can ita a kwai tsoron masifa, Shahudah kam dama tanada taurin kai tun fil azal, dukda tana a tsorace da sakamakon abinda zai biyo baya wani gefen zuciyarta na nuna mata Jawaad zaiyi buyaginsa naɗan lokacine ya sakko. Wannan gurgun tunanin natane yasa bayan ta farfaɗo daga sumar da tayi saita ragema kanta fargabar. Sunata ƙulla mafitar da zasu kare kansu ne a wajen Jay tun bayan farfadowar Shahudah, a wannan yanayin ne motar Jawaad data security's ɗinsa suka iso gidan. Takun takalmansu Jawaad ya sakasu Mummy zubama ƙofar falon ido, dama Shahudah da Aamilah da Mummy ne kawai a falon, duk da kiran sallar magriba da akayi Mummy ce kawai taje tayi, maimakon taima Aamilah magana tunda ita Shahudah batayi saboda jinin ɓari sai batai ba, itako Aamilah dayake bata da man kai batai ko niyyar tashinba balle tunanin yi, idanma zaka bibiya ƙila yau daga sallar asubahi bata sake wata sallaba. Kamar yanda Qaseem ya ɗorasu a kan keken ɓera koda Jawaad yazo kar wanda ya nuna razana hakan duk suka shirya, sai dai da yake a yanzu basuyi tunanin shi bane sai Aamilah ta miƙe domin duba mai knocking ɗin ƙofar. Sun san dai idan Jawaad ne kansa tsaye zai shigo ciki. Cike da barbaɗa ta buɗe ƙofar tana wani yatsine-yashine, taima Rose kallon sama da ƙasa tana faɗin, "Madam ke kuma fa?". Rose ta nunama Aamilah ID card ɗinta tana faɗa mata suna "Sunana Rose Ayo, ƴar sandar farin kaya". Karaf a kunnen Mummy da Shahudah, dan haka duk suka miƙe suma suna nufo ƙofar. Aamilah data ɗansha jinin jikinta tace, "To lafiya?". "Ai mu dakin gammu kinga lafiya hajiya". 'cewar Rose tana wani annaminin murmushi. Ƙoƙarin fita Shahudah da Mummy sukeyi, hakanne ya saka Rose basu hanya, itama Aamilah saita take musu baya. Dukansu idanunsu akan Jawaad dake jingine da ƙarfen da akai kwalliyar barandar suka sauka, ya harɗe ƙafafu waje guda yana danna waya tamkarma baisan mi akeba. Mummy da jikinta ke tsumar tsoron ganin yanayin Jawaad tace, "My son lafiya kuwa....?" Kansa ya ɗago yana wani kaɗa hannunsa ya matse wayarsa tare da miƙewa tsaye sosai, a kausashe yace, "Ba ɗaba, Jami'in tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya *_JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSUF_* ne wannan, munzo ne domin gayyatar mutane uku na gidannan zasu amsa mana wasu ƴan tambayoyi a office Hajiya". Idanu sosai Mummy ta zaro, Shahudah kam ai neman faɗuwa ƙasa tayi, Rose kuwa dake mata kallon tsana ta tarota tana fadin, "Madam kulafa". Shiko Jawaad ko kallon inda Shahudah take baimayiba dama. Aamilah cikinta kam ya ɗuru ruwa, harta fara ƙaramin fitsari a pant ɗinta😝. Dai-dai nan Jack da Salman suka shigo, dan yajene ya gama shirin jirgin da zai tashi a safiyar gobe dashi zuwa ƙasarsa kamar yanda Qaseem ya bashi shawara, sam basuyi zaton zuwan Jawaad gidan a daren yau ba, ko a ƙofar gida da sukaga motoci basu kawoma ransu shineba tunda shi dai Salman yasan Jawaad baida Securitys. Mummy zata sake magana Jawaad ya daka mata tsawa yana faɗin, "Hajiya nace wannan ba ɗanki bane, jami'in tsarone a gabanki ki kama kanki". Ba Mummy ba hatta dasu Hafislz kansu tsawarsa ta firgitasu, dama tunda suka iso gidan mamaki ya kamasu, dan dai a saninsu wannan gidan Gwaggonsa ce, kuma gidan surukansa. Furicinsa sosai ya sakasu a ruɗani, ya kuma basu umarnin tafiya da Shahudah da jack da Aamilah. Yana gama lissafa da waɗanda za'a tafi ya doshi hanyar barin gidan cikin takun bajinta mai ɗauke da izzar fushi. Gaba ɗaya ji da ganin Mummy sai ya toshe ɗaf, bibiyu ma takoma ganin mutane saboda ruɗani da mamakin Jawaad. Kukan da Aamilah ke yine saboda tafiya da za'ai dasu ya maido Mummy a hayyacinta, duk roƙo da magiyar da takema su Hafiz babu wanda ya saurareta, umarnin boss ɗinsu kawai suke ƙokarin cikawa, duk da zukatansu a ƙulle suke da wannan aiki sukam yau. Lokacinma da suka fito dasu Shahudah tuni Jawaad ya shige mota abinsa, ya lumshe idanunsa da sukai masa nauyi, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa bisa kansa, duk yanda yaso kiyaye irin wannan ranar sai da Shahudah tai ƙoƙarin zuwanta, to lallai kam zai tabbatar musu shi *_ƘWAI cikin ƘAYA_* ne, gashi dai abinso ga kowa, sannan kuma abin haɗari ga kowa, da kayi kuskuren ɗaukarsa kasha sukar ƙaya, ƙilama kana taɓashi ya iya fashe maka. Tsabar ya manna musu hauka cayay a kaisu a ajiye, shiko yace a wuce gida dashi yana buƙatar hutawa.
★★★★★
Ana fita dasu Shahudah Mummy ta zube ƙasa ta fashe da kuka tana ƙwala kiran sunan Jawaad. Salman ne yazo ya ɗagata shi kansa jikinsa sai tsuma yake, gaba ɗaya Jay ya rikiɗe masa a idanu tamkar ba shiba, da ƙyar ya iya taimakawa Mummy ta miƙe suka koma cikin falo. Shine yay ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa, sannan Qaseem daya fita, dan baya gidan komai ya faru. Ya kira Mama Atika ya sanar mata itama. Kafin kace mi komai ya hargitse, magana ta fara fitowa a family house ɗin su Jawaad, dama daga can kuma Maman Zaitun ta kira itama ta sanar da kama Zaitun da akazo akayi ba tare da sunsan mita aikata ba. Lokacin da motar Jawaad ta shigo gaba ɗaya gidan ya ɗauki zafi. Yasan abindama yafi hakan zai faru dan haka ya shiryama kowa a gidan akan wannan case ɗin, kallon wani baiyiba a cikinsu ya shige sashensa ya kulle kansa. Sama ya haye abunsa canma ya kulle har Windows yandama bazaiji kiran waniba a cikinsu, ya kuma kashe duk wayoyinsa suma.
********
Ana cikin haka Mummy da Salman suka iso gidan nasu Jawaad. Yayinda shi kuma Qaseem ya zarce office a tunaninsa Jawaad yana can dasu Aamilah, sai dai ya iske kosu bama akawo canba, kenan wani waje daban yasa aka kaisu?, kuma an tabbatar masa Jawaad bai dawo office ba tun fitar da yay da yamma. A fusace ya nufo gidansu Jawaad ɗin, inda ya iske hankulan kowa na gidan a tashe, duk da dai wasu na dariya a ƙasan rai da jinjina abinda Jawaad ɗin ya aikata a bazata. Duk knocking ƙofar da suke masa baiko motsaba balle suyi tunanin zai buɗe su sami yanda suke buƙata, duk da yana jinsu yay kunnen uwar shegu dasu, wankansa ma yayi, yay shirin kwanciya bayan yayi shafa'i da wutiri, duk da yasan barci da wahala ya ɗaukesa.
Ganin Jawaad yaƙi buɗe ƙofa adaren sukaje suka sanarma kakansa abinda ke faruwa, baiyi mamaki ba, dan dama sune suke ɗaukar Jawaad kamar baisan mi yakeba saboda ya zuma ƴarsu ido tana yanda ta gadama, a gabansu shima ya gwada wayar Jawaad ɗin amma switch up. Numfashi Baba ya sauke a hankali yana faɗin, "Wayarsa a kashe take, gashi nikuma ba ƙafar kirkiba balle nace zanzo gidan a daren nan, muyi haƙuri zuwa safiya za aimasa magana insha ALLAHU zai fidsosu, wauwtace irinta Jawaad kawai". Duk yanda dai suka so ganin su Shahudah basu kwanaba dole suka haƙura tunda babu mafita, aiko ranar anan gidan Mummy ta kwana.
Kamar yanda ya saba yauma sai da ya fita sallar asubahi ya sami salla a cikin jam'i, duk yanda su Uncle Uwaisu sukaso ritsashi basu samu wannan damarba, dan yafisu ƙwarewa a wannan fanin. Cikin nutsuwarsa yay shirin fita tsaf cikin baƙaƙen Suit da rigarsa ta ciki fara, yayi ƙyau dan dama mai ƙyawunne, tun daga falon sama ya hango Suraj cikin samarin gidan yaron Uncle Uwaisu ne, Sai da ya haɗa tea ya sakko ƙasa riƙe dashi a hannu yanata turiri, tunda ya fara sakkowa daga steps ɗin benen Suraj ya zuba masa idanu, komai na Jawaad abin so ne, kodan tarin nutsuwar da ALLAH yay masa. Suraj ya mike domin girmama wa ga Jawaad ɗin, sai da Jay ya zauna a kujera maicin mutum ɗaya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan shima Suraj ɗin ya zauna. "Yah Jay barka da safiya". Jawaad dake juya cokali cikin kofin tea ɗinsa ya amsa a dakensa, "Barka dai Suraj, lafiya dai ko?". Murmushi Suraj yay yana risinar da kai ƙasa, "Lafiya lau Yaya, dama su Abbane sukace na kiraka, wai suna jiranka a sashen Mama". Shiru Jay bai amsaba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, "Tom zanzo". Daga haka yay gum da bakinsa. Mikewa Suraj yay yayi masa sallama ya fita.
Jawaad yaja siririn tsaki yana kai kofin shayinsa a baki, sai da ya kammala shan tea ɗin tas cikin nutsuwa kuma sannan ya miƙe ya fita, dama ko basu kirasa ba yayi niyyar zuwa wajensu.
Kamar yanda ya saba dakewa da shanye ɓacin rai yanzunma hakan yake, ya iso sashen Mama Atika a tsumensa alamun babu wasa ko ɗaukar abinda bai masaba ga kowa. Gayyar Uncle's ɗinsa ya iske a falon mama Atika, harma dasu Mummy, murmushi yayi wanda ya bayyana loɓar kumatunsa duka biyu, wato taron dangi aka shirya masa kenan?. "Duk zan iya daku ai" ya faɗa a fili murya ƙasa-ƙasa yana kaiwa zaune a kujerar da yake ƙyautata zaton dama shi aka barwa. Wata ƴar ƙaramar dariyar muguntar daya tanadar musu yayi a zuciya. Suko maɗaukakin mamaki duk ya bayyana a fuskokinsu, musamman yanda sukaga shi tashi fuskar babu alamun damuwa, saima wani kwarjini da cikar haiba shinfiɗe a kanta. Ya zauna yana ajiye wayoyinsa a ƙaramin tebirin dake gefen kujerar da yake zaune. "ALLAH dai yasa lafiya? Na ganku haka, Barkanku da safiya?". Yay maganar cikin nuna halin ko in kula da kallon ƙurillar da suke binsa dashi su duka. Sosai tambayar rainin hankalinsa ta bugi ƙirazansu, Uncle Nasir yay masa daƙƙuwa yana faɗin, "Kaci gidanku Jawaad, ya kakema nuna kamar bakasan mika aikataba?". Wani murmushi Jawaad ya saki yana harɗe ƙafafu ɗaya bisa ɗaya, da kwantar da bayansa a kujerar, "Uncle minayi nikam?". Dukansu baki suka saki suna kallonsa. A harzuƙe Mummy tace, "Kai mara mutunci, bama kasan mi kayiba? Kaje har gida ka kama matarka ta sunna da ƴan uwanka amma kake mana wannan rainin hankalin naka?". Jawaad yay wani luuu da idanu da sauke numfashi, ya taɓe baki kaɗan yana ɗaukar wayarsa ɗaya ya shiga latsawa, "Mummy kenan, na dai kama waɗanda suka bada gudun mawar zubarmin ciki da wadda ta aikata zubarwar, ai matar ƙwarai ta sunna data wadatu da tarbiyya koɗan shegene bata zubar dashi balle ɗan halak na sunna. ku sanarmin kawai yanzu ku miya taraku anan?". Mummy data nema zaucewa da kalamun Jawaad zatai magana Uncle Nasir ya katse ta. "Kai Jawaad ka dawo hankalinka kaji, kasan da suwa kake magana bamason takadaranci, kai yanzu kanaga ya dace ace matar aurenkace ta kwana a rufe? koda abinda kake zargi ya faru ai wannan maganace ta cikin gida, miyasa mu bazakazo ka sanar manaba muyima tufƙar hanci?". Shiru kamar Jawaad bazai amsaba, sai kuma ya ajiye wayar da yake dannawar ya maida hankalinsa ga Uncle Nasir yana ƙoƙarin ɗaukar takardar daya ajiye tare da wayoyinsa. "Uncle wannan ba maganar gida bace, yanzu haka badan yinta yasa nazo nanba, dan Office zanje ana jirana, inhar akan maganar yaran canne kuka taru anan to bazaku ji komai daga gareniba, kudai nema lauya kawai, dan sai an biyani cikina, ita kuma da kuke tunanin zan raga mata saboda igiyar auren da bata amfanamin komaiba tunda aka ƙullata to ga shi nan na tsinkata, kucirema zukatanku mutuncina ne zan taɓa saboda ta kwana hannun jami'an tsaro". Babu wanda bai zaro ido waje ba saboda mamakin furucinsa babu ko kunyar ambaton cikinsa da yake. Jikin Uncle Ayuba har ɓari yake wajen ɗaukar takardar da Jawaad ya ajiye ya duba. Cikin tsagwaron tsoro da firgici yace, "Wlhy yayi sakin". Kusan duk a tare suka ce saki kuma?!!!. Jawaad ya tattare wayoyinsa zai miƙe yana katse musu tunani da fadin, "Ku gafarceni zan wuce ana jirana, kuna tunanin zan cigaba da zama da jahilar da sam bata da tarbiyyar addinin islama ne?". "Jawaad yaushe ka zama haka?". Cewar Uncle Sadiqu baki a hangame. Babu ko gezau kuwa Jay ya bashi amsa da, "Uncle ai indai nine na wuce hakan, dama can ƙaramin sani kukaimin shiyyasa". Hannu mama atika da Inno suka saka aka suka fasa kuka, wai Jawaad na musu rashin kunya, ko ubansa Abdul-aziz bazai musu wannan abunba. Haƙuri sukaita basu, Jawaad kam yay shiru uffan bai ceba. Sai da falon ya lafane Uncle Nasir ya kalli Jawaad ɗin ransa a ɓace yace, "Wai shin ko ka fara shaye-shayene bamu saniba? Yanzu kai Jawaad duk yabon hakurinka da ake a gidannan ashe hasashen banza mukeyi?". Jawaad dake ta ƙoƙarin danne fushinsa yay guntun murmushi yana shafa fuskarsa, "Uncle duk yanda zan maka bayani bazaka fahimceni ba, bansan wane irin haƙuri kukeso nayi akan jahilci da rashin tarbiyyar hudah ba, ankai maƙurar da bazan iya ɗaga ƙafaba kona yafe gaskiya, karku saka kanku a wannan rigimar domin tsakanin ni da itane kawai a cikinta". Da yawansu maganganunsa sun shigesu, dan kuwa dai kowa yasan Shahudah kam bata da tarbiyya. Gwaggo Nafisa mahaifiyar Zaitun tace, "To anji rigimarka ce tsakaninka da Shahudah, ita kuma Zaitun da su Aamilah miya kawosu ciki?". Idonsa ya lumshe nanma yana rumtse hannunsa da ƙarfi, ya buɗesu akanta sun kaɗa sunyi jazur, kamar zaiyi magana sai kuma baice komaiba ya miƙe yana kwasar wayoyinsa, dan idan har ya cigaba da zama tabbas zaiyi abinda ba tarbiyyarsa ba. Kamar ruwa ya cinyesu haka falon yay tsitt suka bishi da kallo kawai harya fice. Uwargidan Uncle Nasir ce ta miƙe tana faɗin, "Inhar gaskiya kuke bukata a wannan zancen to yaron nan yafiku gaskiya, mai makon wannan titsiyen da lallaɓashi kukayi yafi, tunda da dai dukanku kunsan gargaɗin da yayma Shahudah tun yunƙurin zubar da cikin nan da tayi na farko, yanzu kuma ta aikata aiko dole ku shirya karɓar abinda yamafi haka daga gareshi". Tana gama faɗa tabar musu falon, bata saurari yanda suka kacame da maida mata murtani ba, duk da sunsan gaskiya ta faɗa a maganarta.
Koda Jawaad suka isa Office hidimar gabansa ya cigaba dayi baiko bi takan su Shahudah ba, waɗanda shi kaɗai yasan inda yasa aka kaisu saiko su Hafiz da suka kaisun. Yayi hakane kuma saboda Qaseem, ilai kuwa ranar Qaseem ɗin yini yay fafutukar bincike nason gano inda Jay yakai su Shahudah ɗin, sai dai ko wata alamar da zai iya samu Jawaad bai bariba. Daga ƙarshe Office ɗin Jawaad ɗin yaje yana masa magana a gadarance. Jawaad yay masa banza kamar baisan kurar daya kwaso Qaseem ba, sai da ya gaji da hayaniyarsa ne ya miƙe yana kallonsa a wulaƙance, "Ni bani da lokacin yin magana da kowa akan wannan batun, kuje ku nema lauya zuwa gobe zamu shiga kotu". Aiko jin haka Qaseem ya kuma haukacewa da surutai, sai Jawaad ɗinne ya bar masa Office ɗin.
Duk yanda sukaso zama da Jawaad akan a sasanta sam yaƙi basu hadin kai, ranarma bai kwana a gidanba, a gidansa yaje ya kwana, da yake yanzu su Aliyu kowa ya koma gidansa wajen iyalinsa. Su kansu su Hafiz ɗin yaki sanar musu abinda ke faruwa, duk tambayar da suke masa akan kama su Shahudah sai dai yace suyi hakuri subar maganar. Daga ƙarshe dole suka ƙyalesa saboda basa bukatar shiga haƙƙinsa. Dai dai da kakansa yaki yarda su haɗu, hakama su Umma sunbi duk hanyar da zasu gansa akan maganar ya tosheta, yaƙi sauraren kowa, yakumaki faɗama kowa ina su Shahudah suke.
Wannan abu ba ƙaramin tada hankalin Mummy yayiba, ga Abba bai dawoba dukda shima acan hankalin nasa a tashe yake, ya gwada kiran Jawaad ɗin amma saiya iske ya sakashi a black list shima. Kamar wasa saiga su Shahudah na neman rufa sati guda ba'asan inda sukeba, Jawaad yakumayi finfiris yanata aikin gabansa hankali kwance, dan yama cirema kansa damuwar cikin acewarsa ALLAH yasa haka shine yafi alkairi.
Lokacin da ake wannan dambarwar kam Bilkisu na makaranta abinta hankali kwance suna shirye-shiryen fara zana jarabawa.
_________________________ BILKEESU _________________________
Komai na fara zana jarabawarmu ya kammala, dan haka muka ajiye duk wani shiririta muka sake maida hankalinmu a wajen karatu. Musamman ma ni danafi kowa buƙatar ƙarin haske akan komai, sai dai yanda su Zuhrah ke ƙaramin ƙwarin gwiwa yasa bana tare da wani tsoro ko fargaba, da ai banyi tunanin zuwa wannan matsayinba, ALLAH ya kawoni kuma ai bai kamata na sakama kaina tunanin rashin nasara ba. A wannan yanayin muka fara zana jarabawar mu...........✍🏻
*_BAYAN SATI UKU😒_*
*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279 _MARYAM SANI_ _ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇 *07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/HFjVgQVnmn0
*_MANHA HAUSA NOVEL'S_*👆🏻